Connect with us

Siyasa

Mambobin majalisar dokokin Kano 11 sun fice daga jam’iyyar PDP

Mambobin majalisar dokokin jihar Kano 11, sun sauya sheƙa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai mulki da kuma sabuwar jam’iyyar NNPP.

A kwanakin baya ne majalisar ta sanar da sauyin sheƙa da wakilin ƙaramar hukumar Birnin Kano a zauren ya yi watau Salisu Maje Ahmad Gwangwazo daga PDP zuwa jam’iyyar APC.

Sai ga shi a yau Juma’a ma sakataren yaɗa labarai na majalisar Uba Abdullahi ya sanar da sake ficewar mambobi 10 daga PDP zuwa jam’iyyar NNPP.

Waɗanda suka sauya sheƙa a yau sun haɗa da:

1. Rt Hon. Isyaku Ali Danja wakilin ƙaramar hukumar Gezawa.

2. Hon. Umar Musa Gama wakilin mazaɓar Nassarawa.

3. Hon Aminu Sa’adu Ungogo na ƙaramar hukumar Ungogo.

4. Hon Lawan Hussain Chediyar Ƴan Gurasa wakilin mutanen Dala zauren.

5. Hon. Tukur Muhd mai wakiltar Fagge.

6. Hon.Mu’azzam El-Yaku na Dawakin Kudu.

7. Hon. Garba Shehu Fammar wakilin Kibiya.

8.. Hon. Abubakar Uba Galadima na Bebeji.

9. Hon Mudassir Ibrahim Zawaciki na Kumbotso.

10. Hon Sulaiman Babangida mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwale.

Haka kuma sanarwar ta ruwaito cewa dukkan waɗannan mambobi sun gabatar wa majalisar takardar shaidar sauyin jam’iyya.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet