Labarai
Tsagin Ganduje ya yi nasara a kan na Shekarau a kotun ƙoli

A yau Juma’a ne kotun ƙolin Najeriya ta yi watsi da ƙarar da ɓangaren Malam Ibrahim Shekarau na jam’iyyar APC suka shigar a kan tsagin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar a Kano.
Kotun ƙolin ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wadda ta bai wa ɓangaren Ganduje shugabancin jam’iyyar APC a Kano inda ta tabbatar da zaɓen da ɓangaren gwamnan suka gudanar.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, yayin yanke hukuncin, kotun kolin mai alƙalai biyar ta yanke wanda mai shari’a Ibrahim Saulawa ya sanar, kotun ta ce, babbar kotun birnin tarayya Abuja ba ta da hurumin yin shari’ar a matakin farko.