Labarai
Jam’iyyar APC ta yi rashin mambobi 3 a majalisar dokokin Kano

Mambobin majalisar dokokin jihar Kano guda uku, sun sauya sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa sabuwar jam’iyyar NNPP.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na majalisar Uba Abdullahi ya fitar a Larabar nan, Majalisar ta bayyana cewa mambobin ƙananan hukumomin sun gabatar mata da takardar su ta sauyin jam’iyyar.
Haka kuma sanarwar ta ce, mambobin da suka sauya jam’iyyar sun haɗa da: mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Abdullahi Iliyasu Yaryasa mai wakiltar ƙaramar hukumar Tudun Wada sai Muhammad Bello Butu-Butu wakilin ƙananan hukumomin Rimin Gado da Tofa da kuma Kabiru Ismail mai wakiltar ƙaramar hukumar Madobi.
Wannan sauya sheƙa dai na zuwa ne kwanaki biyar bayan da ƴan majalisar 10 na jam’iyyar PDP suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ta NNPP.
Yanzu haka dai a zauren majalisar dokokin ta Kano jam’iyyar APC mai mulki na da mambobi 26 sai NNPP da ke da 13 yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ke da mutum ɗaya.