Tsaro
Bayan rikiɗewar zanga-zanga zuwa tarzoma, Gwamnatin Sokoto ta sanya dokar hana fita

Gwamnatin Jihar Sokoto, ta sanar da sanya dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a faɗin jihar.
Hakan dai na cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Facebook.
Haka kuma a cewar sanarwar dokar za ta fara aiki nan take daga lokacin wallafa ta.
Gwamnatin ta Sokoto ta kuma bayyana cewa ta ɗauki matakin ne biyo bayan rikiɗewar zanga-zanga lumanar da matasa suka fara yi zuwa tarzoma.
Haka kuma gwamnatin ta ce, ta ɗauki matakin sanya dokar ne dawo da zaman lafiya a jihar tare da tabbatar da cewa mutane sun bi doka da oda.
Da tsakar ranar yau Asabar ne matasan suka fara gudanar da zanga-zangar da nufin neman jami’an tsaro su saki matasan da suka cafke su bisa zargin su da hannu wajen hallaka ɗalibar da ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu Tsira da Aminci su tabbata a gare shi.