Featured
Siyasar Kano: Nasiru Gawuna da ƙalubalen da ke gabansa

Ba ina nufin duk faɗn jihar Kano babu wanda ya cancanci zama gwamnan kamar Gawuna ba. Amma dai iya fahimtata a cikin waɗanda suka nuna kwaɗayinsu na ɗarewa kujarar gwamnan a wannan zubin a kuma dukkanin jam’iyyun , babu wanda yake da dama-dama kamar sa. A tashin farko bayan ayyana sunan nasa a matsayin wanda gwamna Ganduje ya amince ya gaje shi . Na taya Kanawa murna saboda samun mutumin da mafiya rinjaye na al’umma suke yi wa shaida da mutumin kirki. Mai mutunta jama’a da kame kai. Wanda da alama idan ya ɗare kujerar gwamna zai nuna haziƙanci da nuna ƙarewa a karagar mulkin Kano.
Sai dai kash! Kafin tafiya ta yi nisa, sai shi mai gayya mai aiki wato gwamna Ganduje ya ɓata rawarsa da tsalle. Inda ya yi ragon azanci wajen kasa jawo jiga-jigan ƴan siyasar da ake ganin ba kanwar lasa ba ne a siyasar jihar Kano a jiki. Maimakon haka sai ya rungumi tare da fifita waɗanda ake gani ko akwatunan unguwanninsu ba za su iya tsira da su ba. Rashin bai wa Sanata Mallam Ibrahim Shekarau damar komawa kujerarsa, da kuma bai wa Sanata Kabiru Gaya takara maimakon Kawu sumaila ba ƙaramin kuskure ba ne. Rashin kula wa da buƙatun Malam Salihu Sagir Takai zai jawo matsala a tafiyar. Domin shi ma yana dab da canja sheƙa.
Fitar da dama daga ƴan Majalisun Jiha da na Tarayya da wasu Shugabannin Kananan Hukumomi daga jam’iyya mai ci idan wa’adin mulki ya zo ƙarshe daman wannan ba wani abin mamaki ba ne. Haka dimokaraɗiyyar zamani ta gada, duk wanda bai sami takara ba zai iya canja sheƙa. Tun da daman su ƴan siyasa ba malam talaka ke gabansu ba illa muƙamin da za su samu.
Takarar Nasiru Yusif Gawuna don zama gwamnan Kano wanda zai gaji gwamna Abdullahi Umar Ganduje za ta sami tasgaro da tirjiya da zafaffiyar hamayya wanda da kyar a iya kai wa gaci saboda dalilai da dama:
1. Daman a zaɓen da a ka yi na gwamna Abdullahi Umar Ganduje a 2019 alƙaluman zaɓe sun nuna jam’iyyar PDP wacce take da ɗan takara Abba K Yusuf, ita ce ta lashe zaɓen. Idan masu bibiyar shafina ba su manta ba har na fito fili na taya jam’iyyar PDP murnar cin zaɓe a wancan lokacin sai kwatsam a ka sami abin da a turanci suke kira wai INKWANKULUSIF ta faru. Ba zan yi doguwar magana a kan wannan ba, domin an san me ya faru.
2. A zaɓukan 2015 da 2019 jam’iyyar APC ta fake ƙarƙashin inuwar ƙauna da farin jinin shugaba BUHARI wajen cin zaɓe. Yanzu kuwa kowa ya gane gaskiyar lamari. Hatta ƴan jam’iyyar APC ɗin ma, ba su son haɗa hotonsu da na Buharin. Ballantana a nemi tabarruki. Kenan Gawuna ba zai sami wannan garaɓasar da ƴan baya suka samu ba. Wato yanzu kowa tasa ta fishshe shi.
3. Kalaman da ya yi a wani jawabi bayan an ayyana shi a matsayin ɗan takarar gwamna a zaɓe mai zuwa. Ya yi wani bayani inda ya ce,’ lallai zai riƙe alƙawarin gwamna, kuma zai yi irin tafiyar da Gandujen yake so.’ Wannan magana ta yamutsa hazo ta tayar da ƙura. Ta kuma zama abin tattaunawa a bakunan Kanawan Dabo. Dalili kuwa kowa ya san ƙaurin suna da gwamna ya yi wajen babakere a harkar ƙasa da tsundumar iyalinsa cikin harkar filaye dumu-dumu. Hakanan da kuma zargin karɓar rashawa da ya yi wacce al’ummar Kano ba za su manta da shi ba, abin da ya jawo wa gwamna baƙin jini da fushin Kanawa.
4. Matuƙar ba a sami sasanci nan da wasu ƴan kwanaki masu zuwa ba. Za a fuskanci ficewar jiga-jigan ƴan siyasa guda biyu daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar NNPP wacce tsohon gwaman Kwankwso yake jagoranta. Malam Salihu Sagir Takai da Malam Ibrahim Shekaru kowannensu yana ta tattaunawa da magoya bayansa domin yanke hukuncin ficewa daga jam’iyyar ta APC. Lokaci ba ya jira alamu na nuna duk ɓangaren da ya sami shawo kan waɗannan jiga-jigai guda biyu ka iya lashe zaɓe cikin lumana.
Waɗannan dalilai da ma wasun su da ban kawo su ba suna nuna matuƙar gwamna Ganduje bai yi saurin gyara kurakurrnsa cikin satin nan ba, to kuwa ba zai sami magaji ba.
A daren jiya dai mun ji gwamnan ya fara gyara taɓargazarsa inda ya mayar wa da Sanata Barau Jibrin da kujerarsa ta Sanatan Kano ta Arewa, wacce aka ce gwamnan ita yake son ɗarewa.
Allah Ya zaɓa mana shugabanni na ƙwarai masu kishin al’umma a dukkanin matakai, ameen.
Ado Abdullahi ya rubuto daga jihar Kano -Nijeriya