Labarai
Kano: Fashewar wani abu ta jikkata ɗalibai da dama a Sabon Gari

Ana fargabar yara ɗalibai sun jikkata sakamakon fashewar wani abu a unguwar Sabon Gari da ke Kano.
Rahotonni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa wani ganau da ya tabbatar mata da faruwar lamarin ya ce, fashewar ta faru ne a titin Aba by Court road.
Haka kuma rahotonni sun ce, fashewar ta faru ne a kusa da wata makaranta lamarin da ya jikkata ɗalibai da dama har ma ake fargabar an samu asarar rai.