Connect with us

Labarai

Bayan cafke Ahmed Idris, Gwamnatin tarayya ta naɗa Akanta Janar na riƙo

Gwamnatin tarayya, ta naɗa Mista Anamekwe Chukwunyere Nwabuoku a matsayin wanda zai ci gaba da kula da ofishin Akanta Janar na tarayya bisa   binciken da hukumar EFCC ke yi a kan  dakataccen Akanta Janar Ahmed Idris

Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Aliyu Ahmed, Babban Sakataren ma’aikatar Kuɗi, Kasafin da Tsare-tsare ta na Najeriya.

Sanarwar mai ɗauke da kwanan watan 20 ga wannan watan da muke ciki na Mayu, ta yi fatan Mista Anamekwe zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya da amana da kuma bin dokoki da kuma kwarewa.

A makon jiya ne dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta cafke Ahmed Idris bisa zarginsa da almundahanar kuɗi har naira biliyan 80.

Haka kuma, bayan cafke shi ɗin ne gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da shi daga muƙaminsa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet