Wasanni
Da ɗumi-ɗumi: Manchester City ta lashe gasar Premier

Bayan lallasa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa da ci 3 da 2, ƙungiyar Manchester City ta lashe gasar Premier ta Burtaniya.
Ƙungiyar Manchester City dai, ta samu wannan nasara ne a wasan ƙarshe da suka buga na gasar da yammacin yau Lahadi.
Haka zalika ƙungiyar ta kai ga samun wannan dama ne ta lashe Kasar ta kakar 2021 zuwa 2022 bayan da ta buga wasanni har guda 38.