Labarai
Ƙungiyoyin kishin Arewa sun buƙaci a ɗauki matakan dakatar da ɓarnar IPOB

Gamayyar ƙungiyoyin Farar-Hula a Arewacin Najeriya sun ja hankalin Shugabannin yankunan Arewa da na Kudanci Najeriya da kuma gwamnatin tarayya kan su dauki matakan kawo ƙarshen kashe-kashen da ƙungiyar tsagerun ƴan ƙabilar Igbo IPOB ke yi wa ƴan Arewa mazauna yankin Kudu maso gabashin na Najeriya.
BBC ta ruwaito cewa wannan dai na zuwa ne bayan da a farkon makonan nan da muke ciki wasu ƴan bindiga suka kashe wata mata Harira da ƴaƴanta 4 da kuma ƙarin wasu mutane ƴan Arewa da ke gudanar da sana’o’i a jihar Anambra.
Mijin matar ya shaida wa BBC cewa ɓata garin sun kashe matar tasa mai ɗauke da juna biyu na wata 9 da ƴaƴansa 4 mata.
Haka kuma ya ƙara da cewa an hallaka su ne lokacin da suke kan hanyar su ta dawowa daga ziyarar da suka kai yankin Orumba ta Arewa a jihar Anambra.