Labarai
Daliget Ba A San Halinku Ba: Bashir Ahmad ya sha kaye a zaɓen fidda gwani

Tsohon Mataimaki na musamman ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Malam Bashir Ahmad, ya rasa tikitin takarar jam’iyyar APC na majalisar wakilai a mazaɓar Gaya,Ajingi da Albasu a jihar Kano.
Ahmad ya fafata da ɗan majalisa mai ci a mazaɓar, Abdullahi Mahmud Gaya.
Sakamakon da aka sanar a daren Juma’a ya nuna cewa Bashir Ahmad ɗin ya samu kuri’u 16 kacal, yayin da Gaya ya samu kuri’u 109.
Yanzu dai Mahmoud Gaya ya samu tikitin jam’iyya mai mulki ta APC na neman wa’adi a karo na biyu a zaɓen shekarar 2023.
A lokacin da ake tsaka da gudanar da zaɓen Bashir Ahmad ya bar gurin da ake yin zaɓen na fidda-gwani tun kafin a kammala shi.
Daga nan sai ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa: “A matsayina na mai son tsayawa takara, na bar wurin zaben fidda-gwani na mazabar Gaya, Ajingi da Albasu na tarayya, saboda barazanar rashin tsaro a kan wakilanmu. Idan a na son a yi zaɓe sahihi to kada a yi amfani da ƴan daba,”