Jami’in hulda da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya sanar hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai da yammacin ranar Asabar.
Sanarwar ta ce, “an kama wanda ake zargin ne mai suna Ibrahim Usman mai shekaru 34 wanda yazo kano da daga karamar hukumar Zaria da ke jihar Kaduna a ranar 31 ga watan biyar na 2022 a lokacin da yan sandan Kan Kace Kwabo ke aikin sintinri a kan titin BUK da ke jihar ta kano.”
Haka kuma ta cikin sanarwar SP Kiyawa ya ƙara da cewa “Bayan fara gudanar da bincike ne aka gano wanda ake zargin ya ɗakko motar ne daga wurin da aka ajiye ta a titin Madobi da ke yankin ƙaramar hukumar Kunbotso”.
Haka kuma ya ce, “ A baya an taɓa kai wanda ake zargin gaban kotu da rin wannan zargin na satar mota.”
Haka dai sanarwa ta ce, “Bayan faɗaɗa bincike an kama wani mutum mai suna Hamisu Ibrahim, mai shekaru 55 mazaunin unguwar Sharada, wanda ke haɗa mukullin da ake kira Master Key har guda 29 da ake bude motoci da su”.
Rundnar yan sandan ta kuma ce da aka cigaba da bincike an gano lambobin motoci har guda tara a gunsa.
