Labarai
Fitar ɗan takara: Shugaba Buhari na ganawa da gwamnonin Arewa

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yana gudanar da wata ganawa da gwamnonin yankin Arewacin Najeriya dangane da batun fitar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC.
Wannan ganawa dai na zuwa ne bayan da ake shirye-shiryen gudanar da zaɓen fitar da gwani da zai yi wa jam’iyyar takara a zaɓen baɗi.
Rahotonni sun bayyana cewa, Gwamnonin da su ka halarci taron sun haɗa da Gwamna jihar Kano Dakta Abdullahi Ganduje da gwamna Neja Abubakar Sani Bello da gwamman jihar Borno Babagana Umara Zulum da sauransu.