Siyasa
Kwankwaso ya lashe tikitin zama ɗan takarar shugaban ƙasa a NNPP

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanatan mazaɓar Kano ta tsakiya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya lashe tikitin zama ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar NNPP.
Kwankwanso, ya samu nasarar ne a zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar ta gudanar a yau Laraba.
Kimanin wakilai masu kaɗa ƙuri’a watau Delegate 774 ne da suka fito daga jihohi 36 da kuma birnin tarayya Abuja ne suka zaɓe shi.
Jam’iyyar NNPP dai ta yi taron ne a filin wasa na Moshood Abiola da ke birnin tarayya Abuja.