Labarai
APC: Bola Tinubu na gab da zama ɗan takarar shugaban ƙasa

Bayan kammala tantance akwatuna 10 waɗanda aka kaɗa ƙuri’un zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki.
Alamomi na nuna cewa Bola Ahmed Tinubu na da sama da kashi hamsin cikin ɗari na ƙuri’un da aka tantantace zuwa tsakar ranar yau Laraba.
Sauran waɗanda aka zaɓa ɗin sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasa farfesa Yemi Osinbajo sai tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi da kuma Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan da sauransu.