Labarai
Ƙungiyar ASUU, ta ƙi amincewa da tayin kuɗin tallafi da za a bata

Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU, ta yi watsi da tayin karo-karon kuɗaɗe da za a yi mata don janye yajin aikin da ke yi.
Shugabannin ƙungiyar ne dai suka bayyana ƙin amince bisa yadda mutane za su haɗa kuɗin domin biyan buƙatun da suka sabbaba tsundumar ƙungiyar yajin aikin sai baba ta gani
A yau Asabar ne dai aka yi wa shugabannin wannan gwaggwaban tayi wanda suka sa ƙafa suka yi fatali da shi.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa an yi wa ƙungiyar ASUU tayin ne ta cikin shirin Brekete Family wanda gidan rediyon Human Rights ke gabatarwa a birnin tarayya Abuja.
Rahotonni sun bayyana cewa, Yayin shirin an tattauna da Shugaban ƙungiyar ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke da sauran jiga-jiganta domin shaida wa ƴan Najeriya dalili ƙin janye yajin aikin.
Haka kuma jaridar ta ruwaito cewa, Tun da fari dai mai gabatar da shirin Ahmed Isah, ya kafa asusun tattara wa ƙungiyar kuɗi don kawo ƙarshen yajin aikin.
Haka kuma yayin tattaunawar ta yau jagoran shirin ya gabatar wa ƙungiyar da naira miliyan hamsin wadda Gwamnan Jihar Akwa-Ibom Udom Emmanuel, ya bada a matsayin gudunmawarsa da za a sanya a asusun bankin da aka buɗe domin tara kuɗin.
To sai dai nuna kuɗin ke da wuya sai shugaban ASUU ya nesanta ƙungiyar tasu da kuɗaɗen da ake tarawa ɗin.
Haka kuma Solacebase ta ce, kalama na shugaban ASUU, sun sanya mai gabatar da shirin yin barazanar dakatar da gidauniyar tunda kungiyar ba ta buƙata.