Tsaro
Kano: Ƴan sanda sun cafke mutane 11 bisa rikicin daba

Runadanar ƴan sandan jihar Kano, ta ce ta cafke mutane goma sha ɗaya bisa zargin su da hannu wajen haddasa wani faɗan daba a unguwar Jakara.
Jami’’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya shaida wa manema labarai batun cafke mutanen a Juma’a nan.
Ya ce, bayan faruwar lamarin rundunar ta sami rahoton sirri daga mutane akan wanda keda hannu kan faruwar lamarin wanda ya kai ga cafke wadanda ake zargin.
Haka kuma ya ƙara da cewa kwamd
Rundunar ƙarƙashin kwamishina Samaila Shuaibu Dikko yi nasarar shawo kan matsalar inda ta umarci Baturen ƴan sanda na Jakara CSP Umar Faruk da ya tattara masu ruwa da tsaki na unguwar domin yi musu sulhu.