Labarai
Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Kano

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, zai kai ziyara jihar Kano a gobe Alhamis 16 ga watan Yuni.
Hakan na cikin saƙon da mai taimaka wa shugaban ƙasar Malam Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a yau Laraba.
Bashir Ahmad ta cikin saƙon nasa ya ce shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai je jihar Kano ne domin halartar taron bikin yaye sabbabbin jami’an ƴan sanda a kwalejin horas da ƴan sandan da ke garin Wudil.