Labarai
Katsina: Hukumar Customs ta cafke kayan fasa ƙwauri na fiye da miliyan 38

Hukumar yaƙi da fasa ƙwauri ta Najeriya Customs, ta ce jami’anta sun samu nasarar cafke kayayyaki da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba wanda kuɗinsu ya kai kimanin Naira miliyan talatin da takwas da dubu ɗari biyar.
Babban jami’in da ke kula da ofishin hukumar a Jihar Katsina, Dalhatu Wada Chedi, ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da manema labarai yau a Katsina.
Ya ce, masu kayan sun biya kimanin Naira miliyan 38 a cikin wannan watan da muke ciki na Yuni.
Dalhatu Wada Chedi, ya kuma ce yawan kayan da ake shigarwa da fitarwa ta kan iyakar Jibia cikin watan da ya gabata bayan buɗe kan Iyakar, sun haɗa tan dubu huɗu na gas ɗin girki da tan dubu ɗaya na siminti.