Labarai
Benue: Ƴan sanda sun cafke mutane 4 bisa zargin su da kai harin ta’addanci

Rundunar ƴan sandan ta jihar Biniwe, ta kuma ce ta haɗa kai da sauran jami’an tsaro yayin cafke ɓata garin.
Mai magana ya yawun rundunar ƴan sandan ya ƙara da cewa an kama waɗanda ake zargin ne shekaran jiya Laraba.
Haka kuma ya ce, rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da cewa ta cafke dukkan masu hannu a kai harin.
A ranar Lahadin da ta gabata ne mahara suka kai farmaki ƙauyen inda suka hallaka mutane goma sha biyar tare da ƙone gidaje da dama.