Wasanni
Ɗan wasa Fabio Viera ya sauya sheƙa daga FC Porto zuwa Arsenal

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta kammala cinikin ɗan wasa Fabio Viera daga FC Porto.
BBC ta ruwaito cewa ɗan wasan ya amince da komawa tawagar ta Arsenal ne bisa yarjeniyar cewa zai jima yana buga musu wasa.
Haka kuma ta ruwaito cewa ɗan wasan mai shekaru ashirin da biyu a duniya, ya buga wa tsohuwar ƙungiyar da ya bari watau FC wasanni 54 wadda a nan ya fara harkar ƙwallon ƙafa a watan Yunin shekerar 2020.
Ɗan wasa Fabio Viera wanda kuma ke buga wa tawagar ƴan ƙasar Portugal ta ƴan ƙasa da shekaru 21 ya ci wa ƙungiyar ƙwallaye goma sha uku a wasanni ashirin da ɗaya.
Rahotonni sun bayyana cewa Fabio Viera zai sanya riga mai lamba 21 ne a tawagar ta Arsenal.