Labarai
Bauchi: Ƴan sanda sun tabbatar da kuɓutar tsofaffin Shugabannin hukuma NFF daga masu garkuwa

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, ta ce, masu garkuwa da mutane sun saki tsofaffin Shugabannin hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Ahmed Wakil, ne bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai da tsakar ranar yau Talata.
A cewarsa tsohon babban Sakataren hukumar ta NFF Sani Ahmed Toro, da sauran mutanen da ɓata garin suka yi garkuwa da su sun shaƙi iskar ƴanci.
Haka kuma ya ƙara da cewa, rundunar na ci gaba da tattara bayanai kuma za ta magantu a nan gaba.
Sai dai har kawo yanzu babu tabbacin cewa ko an biya kuɗin fansa gaban in sakin nasu kamar yadda waɗanda suka yi garkuwa da su suka buƙata tun bayan da suka sace su.
BBC ta ruwaito cewa a ƙarshen makon da ya gabata ne aka yi garkuwa da Toro da tare da tsohon mai horas da ƴan wasan Najeriya ƴan kasa da shekara 23 Garba Ila da Isah Ja, a kan haryarsu ta zuwa Bauchi daga birnin tarayya Abuja.