Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Ma’aikatan hukumar NAFDAC sun tsunduma yajin aiki
Ma’aikatan hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya NAFDAC, sun tsunduma yajin aiki bisa rashin biyan su albashi.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, ma’aikatan waɗanda ke ƙarƙashin ƙungiyar ma’aikatan lafiya na Najeriya MHWUN, sun sanar da tafiya yajin aikin ne a yau Laraba.
Shugaban ƙungiyar Auwalu Yusuf Kiyawa, ne ya sanar da fara yajin aikin ma’aikatan, ga manema labarai a birnin Lagos.
Haka kuma ya ƙara da cewa, mambobin ba za su janye yajin aikin ba har sai an biya su.