Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta ce, ta cafke kimanin Tan ɗaya da ɗigo na kayan maye a jihar Katsina.
Shugaban hukumar shiyyar Katsina Mohammed Bashir Ibrahim, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Litinin yana mai cewa hukumar ta samu wannan nasara ne a ƴan watannin baya.
Haka kuma ya ƙara da cewa, sun cafke mutane ɗari biyar bisa zarginsu da safarar ƙwayoyi.
Mohammed Bashir Ibrahim, ya ƙara da cewa, akwai mutane ɗari uku da tamanin da takwas waɗanda suke tu’ammali da miyagun ƙwayoyi, wanda a yanzu haka sun daina bayan da aka basu kulawa, amma a cikinsu har yanzu akwai matasa goma sha tara da har yanzu ake ci gaba da kula da su a cibiyar gyaran hali.
