Labarai
Ƴan bindiga sun kai wa motocin shugaba Buhari hari

Wasu ƴan bindiga, sun bude wuta kan ayarin motocin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da aka tura su mahaifarsa Daura, kafin zuwan shugaban domin gudanar da bikin Sallah.
Rahotonni sun bayyana cewa ɓata garin sun farmaki tawagar ne a kusa da garin Dutsinma na jihar Katsina inda yanzu haka mutane biyu ke karɓar magani sakamakon rauni kan da suka samu.
Ƴan bindigar dai sun kai harin ga motocin waɗanda suke ɗauke da jami’an tsaro da ƴan tawagar shugaban kasa da suka hada da Protocol da kuma jami’an yaɗa labarai.
A wata sanarwa da ya fitar, mai taimaka wa shugaba Buhari kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu l, ya yaba wa jami’an tsaron fadar shugaban ƙasa bisa nasarar da suka yi ta daƙile harin.
Haka kuma, fadar shugaban ƙasa ta bayyana harin a matsayin abun takaici.