Connect with us

Ilimi

An Baiwa Daliban Jihar Kano Hutun Makaranta Na Tsahon Kwanaki 10

Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta amince da hutun kwana 10 na babbar Sallah ga daukacin makarantun firamare na gwamnati da masu zaman kansu da na gaba da sakandare a jihar.

Iyaye da Masu kula da Almajirai da Daliban makarantun su lura cewa hutun zai fara ne daga ranar Alhamis 7 gzuwa ranar Lahadi 17 ga Yuli, na shekarar 2022.

Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar Aliyu Yusuf ya fitar, ka rabawa manema labarai a ranar Larabar nan.

Sanarwar ta ce, Don haka ma’aikatar ta umurci duk daliban SS3 da ke rubuta jarabawar NECO da NABTEB da NBAIS da kuma daliban da ke kan shirin musaya daga wasu jihohi a GSS Gwarzo da GGSS Shekara su ci gaba da zama a makarantunsu.

Hakazalika ma’aikatar ta umurci dukkan manyan malamai da shugabanni da su tabbatar da cewa daliban kwana sun koma makarantunsu a ranar Lahadi 17 ga daliban jeka ka dawo kuma ranar Litinin 18 ga watan Yuli 2022, domin za a fara gudanar da harkokin karatu na yau da kullum a ranar ta Litinin.

Sanarwar ta rawaito, ma’aikatar ta yi gargadin cewa za a dauki matakin ladabtarwa a kan daliban da suka gaza komawa a lokacin.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet