Labarai
Kusan ɗaurarru 600 ne suka tsere daga gidan gyaran hali- Minista

Ministan tsaro na Najeriya Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, ya ce, kusan ɗaurarru ɗari shida ne su ka arce daga gidan gyaran hali na Kuje sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai.
Ministan ya ce, akwai kusan ɗaurarru ɗari uku da su ka miƙa kansu ga mahukunta bayan lafawar harin.
Wasu ƴan bindiga ne dai suka kai hari gidan yari na Kuje a daren Talatar da ta gabata, inda ake zargin cewa ƴan tada ƙayar baya na Boko Haram ne.
Rahotonni sun bayyana cewa an samu mutuwar jami’in hukumar Civil Defence guda.
Haka kuma harin ya yi sanadiyyar lalata ababen hawa da wasu ɓangarori na gidan gyaran halin.