Labarai
Shugaba Buhari Ya Ziyarci Gidan Yarin Kuje,Akan Hanyarsa Ta Fita Daga kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Larabar nan ya ziyarci gidan yarin Kuje inda ‘yan ta’adda suka kai hari a ranar Talata.
KAKAKIHAUSA ta rawaito cewa, ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai farmaki gidan gyaran halin a daren ranar Talata, inda suka tarwatsa wasu sassan gidan ta hanyar amfani da karfin tuwo tare da kubutar da fursunoni akalla 600.
Sai dai a ranar Laraba shugaba Buhari ya ziyarci gidan yarin domin tantance irin barnar da aka yi.
Jami’an tsaro da dama da suka hada da DSS da Sojoji da ‘Yan Sanda sun kewaye shi a yayin da ya kai ziyarar.
Shugaban ya duba motocin da suka lalace kuma an zagaya da shi wurin domin tantance abubuwan da suka lalace.
Rahotanni sun bayyana cewa Buhari na kan hanyarsa ta fita ne daga babban birnin tarayya Abuja zuwa wani taro a kasar Senegal amma ya zarce zuwa gidan gyaran halin ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai bai yi wani tsokaci ba kan halin da ake ciki bayan ziyarar tasa.