Labarai
Harin Kuje: Ƴan sanda sun sake cafke wani gudajjen fursuna

Rundunar ƴan sandan Jihar Ogun, ta ce ta cafke wani gudajjen fursuna da ya are daga daya daga gidan gyaran hali na Kuje sakamakon harin ƴan bindiga.
Jami’in hulɗa da jama’a rundunar Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar yau Laraba.
Ta cikin sanarwar, rundunar ta ce, ta cafke mutumin Yakubu Abdulmuni, mai shekara 28.
Haka kuma Oyeyemi, ya ƙara da cewa an kama shi ne sakamakon samun rahoton da ofishin ƴan sanda na Sango Ota ya yi cewa gudajjen yana wurin.