Labarai
Bayan kamma aikin Hajji: Wani Alhajin Gombe ya rasu

Hukumar jin ɗaɗin Alhazai ta Najeriya NAHCON ta tabbatar da mutuwar wani Malamin addinin Musulunci dan asalin jihar Gombe a ƙasa mai tsarki bayan kammala aikin Hajjin bana.
Sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce Sheikh Dakta Abdurrahman Maigona ya rasu ne a asibitin hukumar alhazan kasar, sakamakon gajeriyar jinya
BBC ta ruwaito cewa, Sheikh Dakta Abdurrahman Maigona malami ne a sashen nazarin addinin musulunci a jami’ar jihar Gombe.
Haka kuma ta ƙara da cewa Sheikh Dakta Abdurrahman Maigona na daga cikin tawagar malaman addinin musulunci da hukumar alhazan jihar ta tura domin tunatar da mahajjata a lokacin aikin hajji.