Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Yan sanda sun cafke gudajjen fursunan Kuje a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ta ce, jami’anta sun cafke wani fursunan gidan gyaran hali na Kuje da ya tsere sakamakon harin ƴan bindiga.
Mai magana da yawun rundunar DSP Muhammad Jalige, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitarwa da yammacin yau Litinin.
Ta ciki sanarwar DSP Jalige ya ce, tun da fari, kwamishinan yan sandan jihar Yekini Adio Ayoku, ne ya bai wa baturan ƴan sanda umarnin sanya ido a faɗin jihar.
“Bayan ba da umarnin babban sifeton ƴan sanda Alkali Baba Usman na daƙile ayyukan taaddanci bayan da ƴan ta’adda suka fasa gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja ne aka samu wannan nasara”, inji sanarwar.
Haka kuma sanarwar ta ce, A ranar lahadi 17 ga watan nan da muke ciki na Yuli ne ƴan sandan suka cafke mutumin mai suna Ali Shuaibu mai sheakaru sittin wanda ɗan asalin jihar Kano ne a wani yanki na Kaduna lokacin da yake ƙoƙarin tafiya Kano.