Labarai
Oyo: Ƴan Majalisar dokoki sun tsige mataimakin gwamna

Mambobin Majalisar dokokin jihar Oyo sun tsige mataimakin gwamnan jihar, Rauf Olaniyan.
Ƴan majalisar sun sauke mataimakin gwamnan ne a zaman su na yau Litinin.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Ƴan majalisar sun tsige Mista Rauf Olaniyan ne bisa zarginsa da rashin bin dokoki da kuma ƙa’idojin aiki da kashe kuɗaɗe ba bisa ka’ida ba da kuma ƙarin wasu zarge-zarge.