Labarai
Nasarawa: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan sanda 10

Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne, sun yi garkuwa da wasu jami’an ƴan sandan jihar Nasarawa su goma.
Rahotonni sun bayyana cewa, ɓata garin sun sace jami’an ne a kan hanyar su ta komawa jihar Nasarawa daga aikin zaɓen jihar Osun.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa wani jami’in ɗan sanda ya bayyana cewa an yi garkuwa da jami’an ne a jihar Kogi ranar 17 ga wannan wata da muke ciki na Yuli da misalin ƙarfe 11:05 na na dare a yankin Obajana.
Haka kuma ya ƙara da cewa, tuni aka tura jami’an tsaro domin bin sahun ƴan bindigar tare da cafke su.