Labarai
Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar hana goyo a babur

Gwamnatin tarayyar, ta ce tana duba yuwuwar hana goyon babur a faɗin Najeriya domin daƙile ayyukan masu satar mutane da ƴan ta’adda.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya sanar da hakan ga manema Labaran fadar shugaban ƙasa bayan kammala taron majalisar tsaro wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta yau Alhamis a birnin tarayya Abuja.
BBC ta ruwaito cewa, Ministan wanda ke tare da takwarorinsa na ma’aikatar harkokin cikin gida Rauf Aregbesola da kuma na ma’aikatar kula da harkokin ƴan sanda Alhaji Maigari Dingyadi, ya ce, gwamnati na tunanin hana amfani da baburan da kuma aikin hakar ma’adanai.
Haka kuma ya ce, gwamnatin za ta yi hakan ne domin daƙile hanyoyin da ƴan ta’adda da masu satar mutane ke samun kuɗaɗe da kuma safarar kayayyaki.
Ta kuma ruwaito cewa, Ministan ya ce ɓata garin na yin amfani da baburan wajen kwasar kuɗaɗen da suke samu daga aikin haƙar ma’adanai wajen sayen makamai.