Labarai
Hukumar JAMB ta fitar da mafi ƙarancin maki na Bana da Baɗi

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun Najeriya JAMB, ta fitar da mafi kankantar makin da ake bukata domin samun damar shiga manyan makarantun na zangon karatun Bana da Baɗi watau 2022/2023.
Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede, ne ya bayyana haka, bayan ganawa da shugabannin jami’o’i, da na kwalejojin fasaha da na ilimi na kasar.
Ya ce, kowacce makaranta na da damar saka makin da take bukata har zuwa maki 220.
Haka kuma, Ya ƙara da cewa babu makarantar da za ta ɗauki dalibin da ke da maki ƙasa da wanda hukumar ta ƙayyade.
Hukumar ta JAMB dai ta amince wa kwalejojin fasaha da na ilimi maki 100, yayin da aka amince da mafi kankantar maki 140 ga jami’o’in kasar.