Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta bai wa EFCC umarnin tsare dakataccen babban Akanta Ahmed Idris

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bai wa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC umarnin tsare dakataccen babban akanta Ahmed Idris, da wasu mutane uku bisa zargin su da badakalar Naira Biliyan Dari da tara da miliyan dari hudu.
Kotun dai ta bada umarnin ne a zamanta na yau Juma’a bayan da jami’an hukumar ta EFCC suka gurfanar da su bisa a gabanta.
Jaridar Solacebase, ta ruwaito cewa, an gurfanar da su ne bisa zargin aikata manyan laifuka da suka hadar da satar kudade cin amana da kuma almundahana.