Rahotonni daga jihar Neja na nuni da cewa mutum guda ya rasu kana wasu da dama sun ɓace a ruwa sakamakon kifewar wani Kwale-kwale a kogin Zumba na Jihar.
BBC ta ruwaito cewa jirgin ruwan na ɗauke da ƴan kasuwa su kusan 50.
Haka kuma ta bayyana cewa mutanen da hatsarin ya ritsa da su suna kan hanyar su ne daga Shiroro zuwa kasuwar Kwata a yankin ƙaramar hukumar ta Shiroro.
Rahotonni sun kuma yi nuni da ce mutane shida kaɗai aka ceto cikin fasinjojin jirgin.
Haka kuma kafar ta ruwaito cewa Babban daraktan hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar, Ibrahim Inga, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa bai samu bayanin adadin mutanen da hatsarin ya ritsa da su ba.
