Labarai
Ba zan taɓa saurara wa ƴan bindiga ba- Shugaba Buhari

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce, ba zai taɓa saurara wa ƴan bindiga ba har sai ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da Najeriya ke fuskanta.
Shan alwashin na shugaban ƙasar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu, ya fitar a daren Lahadin nan.
Sanarwar ta ce, manyan hafsoshin tsaron Najeriya suna yin iyakar bakin ƙoƙarinsu wajen kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga.
Haka kuma ta cikin sanarwar, shugaba Muhammadu Buhari, ya jajanta wa tsohon shugaban jam’iyyar PDP Adamu Muazu, bisa hallaka ɗan uwansa da ƴan bindiga suka yi gami da yin garkuwa da ƴar uwarsa.