Kasuwanci
Buhari Ya Nada Mutane 4 A Matsayin Daraktocin Hukumar CBN

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da wasu mutane hudu domin nada su a matsayin wadanda ba na zartarwa ba a matsayin daraktocin babban bankin Najeriya CBN.
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 21 ga watan Yuli kuma shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren taron majalisae a ranar Talatar nan.
Buhari a cikin wasikar, ya ce an gabatar da bukatar ne bisa ga sashi na 10 (3) (a) na dokar babban bankin Najeriya na shekarar 2007.
Wadanda aka nada sun hada da: Farfesa Mike Obadan (Kudu-Kudu), Farfesa Justitia Nnabuko (Kudu maso Gabas), Farfesa Ummu Jalingo (Arewa-maso-Gabas) da Mista Adeola Adetunji (Kudu-Yamma).
(NAN)