Labarai
Sojojin sun gano ƴan matan makarantar Chibok 2 tare da ƴaƴan da suka haifa

Shalkwatar tsaron Najeriya, ta ce, sojoji sun gano wasu mata guda hudu a cikin daji waɗanda biyu daga ciki suka kasance ƴan matan makarantar Sakandaren gwamnati ta Chibok da ƴan Boko Haram suka sace su a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014.
Hakan na ƙunshe ne cikin wani saƙo da shalkwatar ta wallafa a shafinta na Twitter a yau Laraba.
Saƙon ya bayyana cewa, dakarun Bataliya ta 202 ta rundunar soji ne suka kuɓutar da matan kuma ƴan makarantar ta Chibok suna ɗauke ne da ƴaƴan da suka haifa.
Hoton da shalkwatar ta wallafa ya nuna matan riƙe da yaran nasu.
Haka kuma sanarwar ta ce, matan da yaran duk suna wani asibitin sojoji ana duba lafiyarsu.