Labarai
Da ɗumi-ɗumi: Babbar kotun tarayya ta bada belin dakataccen babban Akanta Ahmed Idris

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bada belin dakataccen babban Akanta na Tarayya Ahmed Idris tare da mutanen da ake tuhumar su tare bisa sharuɗan da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gindaya.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, yayin zaman kotun na yau, mai shari’a Adeyemi Ajayi, ya ba da umarnin cewa wadanda ake tuhumar ba za su bar birnin tarayya Abuja ba, kuma idan tafiyar ta zama wajibi sai su nemi izinin kotu ko kuma a soke belin nasu.
Haka kuma, kotun ta bayyana cewa wadanda ake tuhumar za su sanya hannu kan yarjejeniyar cewa za su bi ƙa’idojin belin da EFCC ta gindaya musu.
Mai shari’a Ajayi ya kuma ba da umarnin cewa mutanen da ake tuhumar kada su yi fasfo na daban ba har sai an kammala shari’ar, bayan sun ajiye fasfo dinsu na asali ga hukumar.
Alkalin kotun ya zatar da hukuncin ne bisa hujjar cewa har yanzu ba a tabbatar da zargin da ake yi wa wadanda ake tuhumar ba.
Alkalin kotun ya zatar da hukuncin ne bisa hujjar cewa har yanzu ba a tabbatar da zargin da ake yi wa wadanda ake tuhumar ba. Kotun ta kuma bayyana cewa, bisa tsarin doka, wadanda ake tuhumar suna da damar bayar da belinsu duk da zargin da ake musu, tun da mai gabatar da kara bai bayyana cewa wadanda ake tuhumar sun aikata ba daidai ba a lokacin da suke hannun EFCC.