Connect with us

Labarai

Dogara, Babachir Sun Yi Wata Ganawar Sirri Da Gwamna Wike

Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC guda biyu, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara a ranar Asabar din nan sun ziyarci gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Mutanen biyu, da isar su, sun shiga wata ganawar sirri a gidan gwamna Wike da ke Fatakwal.

Jim kadan bayan kammala taron, Lawal ya ce sun cika umarnin Littafi Mai Tsarki na ziyartar juna.

“Mun zo ziyarci ɗan’uwanmu,” in ji shi. “Shi ɗan’uwanmu ne kuma a kowane lokaci Littafi Mai Tsarki ya umurce ku da ku ziyarci juna. Abin da muka yi ke nan.”

Dogara ya ce Wike dan siyasa ne ba makawa wanda ya dace da burinsu na gina Najeriya mai dunkulewa.

“Kowa ya yarda da mu cewa Gwamna Wike na daya daga cikin shugabannin siyasa da babu makawa,” in ji Dogara. “Kuma a gare mu, bincuke ya nuna gina Najeriya ta zama dunkulalliyar kasa baki daya. Don haka muna jin cewa a matsayin wani bangare na tsarin ajandar, ya kamata mu gana da shi kuma shi ya sa muka zo nan.”

Kafin ziyarar, a ranar Juma’a Lawal da Dogara, dukkan ‘ya’yan jam’iyyar APC ne suka jagoranci taron Kiristocin Arewacin kasar domin kin amincewa da tikitin jam’iyyarsu ta Musulmi da Musulmi.

A halin da ake ciki, gwamna Wike a ranar Juma’a ya kuma soki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa, Atiku Abubakar, duk da cewa ya sha alwashin ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ta PDP.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet