Siyasa
Takarar mu da Atiku babbar barazana ce ga APC- Okowa

Gwamnan jihar Delta, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa da zai taya Atiku Abubakar takara a jam’iyyar PDP Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa yin takararsu shi da Atiku babbar barazana ce ga jam’iyyar APC a zaɓen baɗi.
Okowa ya furta hakan ne a matsayin martani ga ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC watau Asiwaju Bola Tinubu wanda ya ce, wanda ya zaɓa a matsayin abokin takara ya fi na Atiku.
Haka kuma gwamnan ya ja hankalin Tinubu, kan cewa ya mayar da hankali wajen tattauna batutuwa masu muhimmanci ba na mutum guda ba.
Ifeanyi Okowa, ya ƙara da cewa abinda APC ta yi na zaɓar ɗan takara da mataimaki duk Musulmi ya sake buɗe wa jam’iyyar PDP ƙofar nasara.
Haka kuma gwamnan ya ƙara da cewa, Atiku Abubakar ya zaɓe shi a matsayin abokin takara ne saboda tsabar ƙwarewarsa a siyasa da gudunmawar da ya bayar wajen gina Najeriya ta fuskar riƙe jiharsa cikin aminci a shekaru bakwai na mulkinsa.