Connect with us

Siyasa

Zaɓen 2023: Tinubu zai iya canja Najeriya zuwa sabuwar Dubai- Amb Nuruddeen

Daraktan shiyyar Arewa Maso Yamma na ƙungiyar yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu watau APC Media Mobilization for Bola Ahmed Tinubu, Ambasada Aminu Nuruddeen ya ce, ɗan takarar su na shugaban ƙasa yana da nagartar da ya kamata ya jagoranci Najeriya zuwa ga Tudun mun tsira.

Aminu wanda ya bayyana hakan yau Litinin lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga shugabannin ƙungiyar ƴan jaridar Internet na jihar Kano, ya bayyana cewa ɗan takarar jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya nuna salon jagorancin sa da kuma yadda yake iya gyara rayuwar al’ummar sa a lokacin da yake matsayin gwamnan jihar Kano.

 

A cewarsa, Najeriya na buƙatar shugaban ƙasa kamar Tinubu wanda ke da ƙarewa da hikimar da ba za a iya tantancewa ba don ci gaban Najeriya cikin sauri kuma zai iya mayar da al’ummar Kasar nan zuwa sabuwar Dubai inda kasuwanci da al’ummarta ke bunƙasa.

“Asiwaju Ahmed Tinubu ya ƙirƙiro wa kansa, sunan da ya kamata a riƙa tunawa da shi a duk lokacin da ake maganar ci gaban Legas.

Ya sami damar canja Legas ta hanyar amfani da harajin cikin gida ba tare da jira ko dogaro da sa hannun gwamnatin tarayya ba.

 

A yau Legas ta yi fice a faɗin tarayya saboda irin gudunmawar da ya bayar na kishin ƙasa.

Mutumin da zai iya gudanar da wani wuri kamar Legas cikin nasara, ko shakka babu zai yi matuƙar kyau idan aka ba shi shugabancin Najeriya domin Legas kamar yadda kuka sani ta fi wasu ƙasashe,” inji shi.

Bugu da ƙari, ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar APC ya kewaye kansa da manyan mutane waɗanda za su dafa masa wajen aiwatar da manufofinsa na ci gaba.

“Kuna iya gani daga zaɓinsa na mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shattima, da sauran manyan mutane da ke kewaye da shi, ina tabbatar muku zai yi fiye da yadda ake tsammani”.

Sai dai ya bayyana cewa ƙungiyar matasan ta samar da duk wata hanya ta tallafa wa da kuma wayar da kan al’umma domin samun nasarar jam’iyyar da duk ƴan takararta da ke neman mukaman siyasa a matakin ƙananan hukumomi da ƙasa baki ɗaya.

A nasa ɓangaren, Shugaba na riƙo kuma sakataren ƙungiyar, Yakubu Salisu wanda ya karɓi baƙuncin tawagar, ya bayyana cewa ƙungiyar ta ƙunshi gogaggun ƴan jarida kuma ƙwararru wadanda suka yi aiki da kafafen yaɗa labarai daban-daban.

Ya kuma ba su tabbacin samun cikakken haɗin kan ƙungiyar.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet