Connect with us

Kasuwanci

Obasanjo- Ina shan wuya saboda tsadar da man Dizal ya yi

Tsohon shugaban ƙasa Chief Olusegun Obasanjo, ya koka bisa tashin gwauron zabi da farashin man dizal da kuma farashin abincin dabbobi gami da tashin  farashin canjin suka yi inda hakan ke shafar harkar noman kifi a Najeriya.

BBC ta ruwaito cewa tsohon shugaba wanda manomin kifi ne, ya ce yana cikin tasku bisa tsadar man dizal, kuma hakan na kawo tsaiko ga noman kifinsa.

Haka kuma ta bayyana cewa Obasanjo ya bayyana hakan ne a Talatar makon nan a birnin Abeokuta na jihar Ogun, taron ƙungiar manoman kifi na yankin kudu maso yammacin Najeria a cikin dakin karatun littafi na Obasanjo OOPL.

Obasanjo ya bayyana cewa cigaba da tashin farashin dizel da kuma cigaba da karuwar farashin abincin kifi zai hana manoman yin aikinsu, sai dai in har sun hada kai su amince da farashi da zasu cigaba da barin su suna sana’ar.

Ya yi bayani yana cewa a halin yanzu farashin dizel 800 ne lita daya, sannan samar da kilo daya na kifi naira 1,400 ne, kuma ya kara da cewa, idan har suna son samun riba, to ba za su iya sayar da kifi kasa da 1500, lamarin da ya su duk wani abu da ya yi kasa da haka zai jawo faduwa ne da asara.

Obasanjo ya ce: “Farashin dizel ya yi sama saboda yadda ake tafiyar da kasar nan ba yadda ya dace ba ne.

“Saboda haka idan haka ta faru, wasu daga cikin mu da muke bukatar amfani da dizel domin noman kifi zamu yi asarar ne baki daya, kuma a lokacin da hakan zai faru, ‘yan Najeriya za su ci gaba da bukatar cin kifi.”

“Noman kifi zai gagara, sannan manoman da ke wajen Najeriya zasu ringa kawo wa nan.

“Za ka rasa aikin yi, ka talauce. Saboda haka me ya kamata mu yi? Mu hada kai mu cigaba da raya noman kifi domin kula da bukatun wadanda su ke cin kifi da kuma masu noman kifin,” a cewarsa

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet