Connect with us

Labarai

Hukumar KAROTA ta cafke wani matashi da ya yake sojan gona da kakinta

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta cafke wani matashi da yake yin sojan gona da kakin hukumar.

Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa ya fitar a yau Alhamis.

Sanarwar ta ce, KAROTA ta cafke matashin ne dai-dai lokacin da yake tsaka da tare motoci akan titi da misalin ƙarfe 12:00 na daren ranar Litinin.

Haka kuma hukumar ta ce, Matashin mai suna Lukman Abdullahi mai shekaru 27 mazaunin unguwar Sabon Gari bayan kama shi ya bayyana mata cewa shi ɗan Maiduguri ne.

Ya kuma ƙara da cewa yana amfani da kayan ne saboda jama’a su fahimci shi ma’aikacin hukumar ne.

Mai magana da yawun KAROTA Nabulisi Abubakar kafar Na’isa, ya ƙara da cewa hukumar ta jima da samun rahoton yadda matashin ke amfani da kakinta wajen cusgunawa al’umma, wanda sai a wannan karon dubunsa ta cika.

Sanarwar ta kuma ce, Shugaban Hukumar ta KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya shawarci al’umma da su ci gaba da kai mata rahoton duk wani jami’in da suka ga yana karɓar cin-hanci domin ya fuskanci tuhuma.

Nabulusi ya kara da cewa idan suka kammala binke a kan matashin za su miƙa shi hannun jami’an ƴan sanda domin faɗaɗa bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet