Labarai
Sojoji Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Suna Da Alaka Da Harin Cocin Owo – Janar Irabor

Shedikwatar tsaro ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke ‘yan ta’addan da suka kai hari a cocin St. Francis Catholic Church da je garin Owo, a jihar Ondo.
Babban Hafsan Sojojin Najeriya Janar Lucky Irabor ne ya sanar da hakan a ranar Talata, a wani taro da shugabannin kafafen yada labarai a shedikwatar tsaro da ke Abuja.
Ya ce an kama masu laifin ne tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro.
Kimanin mutane 40 ne suka mutu a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari cocin a ranar 5 ga watan Yuni, inda suka bude wuta kan jama’ar, sannan kuma suka tayar da bama-bamai a yayin da masu ibada suka gudu domin tsira da rayukansu.
(SOLACEBASE)