Ilimi
Hukumar JAMB ta saki sakamakon ɗaliban da suka yi jarrabawar daga baya

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da Sakandare ta Najeriya JAMB, ta saki sakamakon daliban da suka rubuta jarrabawar, daga baya sakamakon samun matsalar da ta hana su yi tare da sauran ɗalibai.
Hukumar ta sanar da sakin sakamakon ne ta cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na hukumar Dakta Fabian Benjamin ya fitar yau Laraba a birnin tarayya Abuja.
Haka kuma ta cikin sanarwar, Dakta Benjamin, ya ce, hukumar ta samar da hanyoyi masu sauƙi da ɗaliban za su bi wajen samun sakamakon nasu ta hanyar tura gajeren saƙon na rubutun RESULT zuwa lambar 55019.
Ya ƙara da cewa, ɗalibai za su iya sauke sakamakon nasu a shafin Internet na hukumar.