Labarai
Kaduna: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da sirikai Farfesa Ango Abdullahi da jikokinsa 4

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da surukar shugaban ƙungiyar dattawan Arewa Farfesa Ango Abdullahi, tare da ƴaƴanta huɗu a yankin ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Farfesa Ango Abdullahi ya tabbatar da hakan ne ga manema labarai a birnin Zaria ranar Larabar makonnan.
Ya ce, ƴan bindigar sun yi garkuwa da matar ɗansa, Ramatu Samaila, tare da jikokinsa su huɗu a daren ranar Talata.
Haka kuma ya ƙara da cewa surukar tasa ƴa ce ga mai unguwar Yakawada.
Rahotonni sun bayyana cewa, ƴan bindigar sun mamaye karamar hukumar Giwa ne ranar Talata inda kai tsaye suka shiga gidan mai unguwar tare da yin garkuwa da wasu mutane a gidan.
Haka kuma ƴan bindigar sun yi garkuwa da mazauna ƙauyen waɗanda suka haɗa da Abubakar Mijinyawa tare da matan sa biyu, Aisha da kuma Hajara dukkan su masu shayarwa.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, A baya dai ƴan bindigar sun yi garkuwa da ɗan Farfesan mai suna Sadiq Ango Abdullahi, a harin jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna amma suka sako shi bayan an biya kuɗin fansa.