Labarai
Allah ya yi wa kakar Abba Gida-gida rasuwa

Allah ya yi wa Hajia Aishatu Ahmad Sufi, kakar ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-gida rasuwa.
Wannan bayanai na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ɗan takarar Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a yau Juma’a.
Sanarwar ta ce Hajia Aisha Sufi, ta rasu ta bar ɗan uwanta Alƙali Hussaini Sufi, tare da ƴaƴanta uku, waɗanda suka haɗa da Malama Khadijatul Najaatu, mahaifiyar Abba Gida Gida.
Jaridar Solacebase ta rawaitu cewa Kakar ta Abba Kabir Yusuf wadda ake yi wa laƙabi da Hajia Mowa, ta rasu yau Juma’a a asibitin koyarwa na Aminu Kano tana da shekaru ɗari da uku a duniya.