Featured
Benzema ne zai lashe kyautar Balland’or ta bana – Kylian Mbappe

Abdu Ado Ƙofar Na’isa
Dan wasa Kylian Mbappe ya bayyana cewar yana goyon bayan abokin wasan sa na kasar Faransa Karim Benzema wajen lashe kyautar Balland’or ta 2022.
Tauraron ɗan wasan Real Madrid Karim Benzema shine dan wasan da akafi ganin ya cancanci lashe kyautar a bana.
Dan wasan mai shekaru 34 ya mamaye komai a Real Madrid bayan abokin wasan sa Cristiano Ronaldo ya matsa daga kungiyar kuma ya jagoranci Real Madrid din ta lashe gasar Laliga, Champions League tare da zura kwallaye 44 da taimako 15 acikin wasanni 46 kacal da ya jagoranci Real Madrid a kakar da ta gabata.
A wata ganawa da gidan jaridar L’Equipe sukayi dashi Mbappe ya tabbatar da cewar yana goyon bayan Benzema ya lashe wannan kyautar kuma yana da kwarin gwiwar shine zai lashe ta.
“Yana da shekaru 34, Kuma kakar data gabata itace mafi kyau a rayuwar sa, Ya lashe gasar zakarun turai,” Haka Mbappe yayi bayani.
“Idan nine Karim, Ko da ban lashe wannan ba, Bazan daina sa ran lashe Balland’or ba har abada.”
Lokacin da ake tambayar sa akan ‘yan wasa ukun da yake ganin zasu zama na farko a wajen lashe gasar, Mbappe ya inganta kansa bayan da ya kare a matsayi na 9 a waccan shekarar.
“Zan iya cewa Benzema, da ni kaina da kuma Sadio Mane,” Haka dan wasan na gaban PSG ya fada.